Ilim public
[search 0]
More
Download the App!
show episodes
 
Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-daban na duniya, tare da nazari kan irin ci gaban da aka samu wajen binciken kimiya da fasaha da ke neman saukakawa Dan’adam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Bil’adama. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe, a ku maimata ranar Alhamis.
  continue reading
 
Artwork

1
Mujer Ilimitada

Abril Falcón

Unsubscribe
Unsubscribe
Monthly
 
"Tu coach para comenzar a ser una mujer ilimitada" Un espacio para hablar sobre el desarrollo personal a partir de experiencias reales, aprendizajes nuevos y como descubrir y entender el poder que tenemos dentro de nosotros mismas.
  continue reading
 
Loading …
show series
 
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako ya duba yadda mallakar takardun kammala karatu na bogi a Najeriya ke barzana ga karewar kwararru a fannoni da dama. Ana fargabar idan har wannan dabi'a ta ci gaba a haka, tabbas za'a rasa kwararru musamman a fannin lafiya, kimiyya da sauransu. Danna Alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Shamsiyya H…
  continue reading
 
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan lokacin ya yi duba ne kan yadda wasu kungiyoyi karkashin cibiyar fasahar sadarwa da ci gaban al’umma wato CITAD suka samar da wata katafariyar cibiyar sadarwa da aka yiwa lakabi da HELLO HOPE a jahar Bauchi. Shirin ya kasance wani bangare na yunkurin saukakawa mazauna karkara hanyoyin samun sadarwa ta internet mu…
  continue reading
 
Matsalar tsaro na daya daga cikin matsalolin da ke addabar Najeriya, musamman ma arewacin kasar, hakan ya sanya sashen koyon aikin jarida na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria da ke jihar Kaduna ya shirya wani taro gagarumin taro na kasa da kasa domin tattaunawa a kan gudumawar da kafafen yada labarai za su iya bayarwa wajen warware matsalar tsaro. Y…
  continue reading
 
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan lokacin ya yi duba ne kan yadda dalibai da dama a Jamhuriyar Nijar, musaman maza ke barin karatu da sunan tafiya neman kudi, kasashen ketare kamar Libiya, Aljeriya ko kuma hako zinare a kasar Mali kai harma da kokarin tsallakawa Turai, abin da ya sanya kungiyoyin dalibai a kasar bazama aikin wayar da kan matasa k…
  continue reading
 
Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon zai yi duba ne kan yadda gwamnatin jahar Neja da ke Arewacin Najeriya, ta samar da shirin horas da dalibai sana'oin hannu don dogaro da kai. Gwamnatin jahar dai ta ware ranar Juma'ar kowane mako don gudanar da darasin koyon sana'oin hannu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsi…
  continue reading
 
A wannan makon zamu duba yadda ci gaban kimiyya da Ilimi ke zama wani nau’I na koma baya musamman a tsakanin dalibai a Najeriya. Tun bayan samar ko kuma kirkirar na’urar kwamfuta a 1837, da kuma shigowar ta Najeriya karon farko a 1963 sannu a hankali take bazuwa tsakanin jama’a, yayi da kuma ake samun ci gaba ta fannin amfani da ita.…
  continue reading
 
Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon zai yi duba ne da tsarin karatun 'yayan makiyaya, wato Nomadic Education. Gwamnatin jihar Neja ce ta yi hobbasa don farfado da shirin karatun 'yayan makiyaya a jihar. Shirin zai bai wa makiyaya damar samun ilimi a duk inda suka yi balaguro don inganta makomarsu. Yanzu haka dai shirye-shirye sun yyi nisa …
  continue reading
 
Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon tare da Shamsiyya Haruna ya maida hankali ne kan nazarin da masana kimiya suka yi wajen kirkirar Tabaraun hangen nesa, don taimakawa masu raunin gani. A jamhuriyar Nijar, matsalar gani na zama babban kalubale ga al'ummar kasar wacce a yanzu har aka fara samunta a tsakanin matasa. Tuni dai matsalar ta san…
  continue reading
 
Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan mako tare da Shamsiyya Haruna ya maida hankali ne kan yadda matsalar tsadar man fetur ke ci gaba da yin tasiri akan harkar ilimi a Najeriya, wanda tun bayan sanar da janye tallafin mai a kasar kanana da manyan makarantu ke daukan matakai daban daban da zummar daidaita harkokinsu a cikin wannan yanayi. Daga cik…
  continue reading
 
Shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan tasirin ilimin fasahar na'ura mai kwakwalwa ko kuma computer ga daliban da ke shirin shiga jami'a a Jamhuriyyar Nijar, sabon tsarin da aka bijiro da shi da nufin taimakawa tarin daliban da basu da gogewa a fannin na fasahar na'urar computer. Wannan mataki dai …
  continue reading
 
Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan mako ya yi duba ne da yada dalibai ke faduwa a jarabawar da ake yi da na'urar komfuta, wato CBT exams. Dallibai dai na yawan kokawa a kaan yadda sukaa faduwa sosai a irin wannan jarabawa, sabanin wadda suka saba, ta alkalami da takarda. Hasali ma daliban naa gaanin cewa matsalar ba daga gare su take ba, inda s…
  continue reading
 
Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon ya mayar da hankali ne kan taron kungiyar malaman jami'o'in shiyyar arewa maso yammacin Najeriya. Makasudin wannan taro kamar yadda kungiyar ta bayyana shine nazari kan irin ci gaban da aka samu ko akasinsa a jam'i'o'in shiyyar da zummar lalubo hanyoyin samun mafita.…
  continue reading
 
Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' ya yi nazarari ne kan cire tallafin mai da sabuwar gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta yi, inda a lokacin da ya ke gabatar da jawabi jim kadan bayan rantsar da shi, Tinubu ya sanar da janye biyan kudin tallafin mai da gwamnatin kasar ke yi, lamarin da ya sa farashin makamashin ya yi tashin gwaur…
  continue reading
 
Shirin wannan mako dai ya yi nazari ne kan fasahar nan ta na'urar da ake sanya wa tunanin dan adam wato Artificial Intelligence, wadda a yanzu hankalin kasashen duniya ya fi karkata akai ganin yadda ya zo da gagarumin sauyi mai ban mamaki. Sai dai duk da ci gaban da wannan fasahar ta zo da shi da ma wanda ake hasashen za ta samar nan da shekaru kad…
  continue reading
 
Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna ya mayar da hankali kan tsarin ilimi ta yanar gizo ko kuma na shafukan Intanet da ake kira da E-Learning ko kuma Digilal Learning. Tun bayan bullar cutar covid-19 ne dalibai da dama suka koma karatu ta yanar gizo ko kuma E-Learning a wani yunkuri na kaucewa ganin karatunsu bai gamu da tangarda ba.…
  continue reading
 
Shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna ya mayar da hankali kan kalubalen da karatun Firamare ke fuskanta a jihar Neja ta tsakiyar Najeriya, dai dai lokacin da ake samu karuwar yaran da ke zuwa makaranta. Mahukuntan jihar Neja sun bayyana cewa adadin daliban da ke shiga Firamare a Neja ya karu daga yara dubu 600 zuwa dubu 800 a bana, sa…
  continue reading
 
Shirin na wannan rana, ya duba halin da karatun daliban da suke tsere daga Sudan ke ciki, yayin da rikici ya barke a kasar da ke gabashin Afirka. Najeriya na daga cikin kasashen da ssuka kwashe dalibai da kuma 'yan kasashen su da ke rayuwa a Sudan, yayin da aka wayi gari da karar harbin bindiga da kuma hare-hare ta sama. Kasar Sudan dai ta fada cik…
  continue reading
 
Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta ce sun fara tattaunawa da mahukuntan kasar Masar a birnin Alkahira, kan yadda za a kwaso daliban kasar daga Sudan, yayin da bangarori biyu ke ci gaba da gwabza yaki a kasar da ke Gabashin Afirka. Wannan ya zo ne, bayan da dubban dalibai 'yan Najeriyar da ke karatu a Sudan suka mika koken su ga gwamna…
  continue reading
 
Loading …

Quick Reference Guide