show episodes
 
Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-daban na duniya, tare da nazari kan irin ci gaban da aka samu wajen binciken kimiya da fasaha da ke neman saukakawa Dan’adam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Bil’adama. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe, a ku maimata ranar Alhamis.
  continue reading
 
Loading …
show series
 
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya yi duba ne a kan yadda matsin tattalin arziki da kuma tsare-tsaren gwamnati suka kassara fannin ilimi a tarayyar Najeriya. Daga ɓangaren mahukunta jami'o'in suna ganin tsare-tsaren da gwamnati ta bullo da su a fannin ilimi sune suka sanya a wannan lokaci ko da gyare-gyare a jami'o'in basa iya aiwatarwa.…
  continue reading
 
Shirin ilimi hasken rayuwa tare da Aisha Shehu Kabara a wannan makon ya mayar da hankali kan tsarin bayar da ilimin Sakandiren kyauta a Ghana, wanda ya taimaka matuka wajen ƙara yawan Ɗaliban da ke halarta karatu a wannan mataki. Duk da cewa shirin ya laƙume kuɗaɗe masu tarin yawa amma gwamnatin ƙasar ta Ghana ta ce ko shakka babu kwalliya ta biya …
  continue reading
 
A wannan mako, shirin ya yi duba ne a kan tsarin dabarun koyo da koyarwa a ƙarni na 21 da ake kira da 21st Century Learning Skills a turance.Tsarin dabarun koyo da koyarwa na ƙarni na 21, an soma amfani da shi tun a shekarar 2001 domin zamanantar da tsarin yadda ake koyarwa ta hanyar samar da dabarun zamani da za su taimaka wa malamai wurin fahimta…
  continue reading
 
Shirin na wannan mako ya mayar da hankali ne kan karuwar matasan da basa zuwa makaranta a Ghana. Hukumar kididdiga ta kasar GSS ta gano cewa kusan matasa miliyan biyu ne ba sa karatun Boko ko aikin yi ko kuma samun horon sana'o'in dogaro da kai. Ku danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abdulkadeer Haladu Kiyawa.…
  continue reading
 
A wannan mako, shirin ya mayar da hankali ne kan yadda tsadar kuɗin wutar lantarki ke gurgunta harkokin karatu a manyan makarantun Najeriya. Kamar yadda aka sani, harkokin gudanarwar yau da kullum na manyan makarantu ba za su taɓa yiwu wa yadda ya kamata ba, muddin babu ingantacciyar wutar lantarki. To sai dai, baya ga rashin tsayayyiyar wutar a ku…
  continue reading
 
A wannan mako, shirin ya yi duba ne a kan yadda hare-haren ‘yan ta’adda suka kassara harkokin ilimi a arewacin Najeriya, shekara 10 kenan da 'yan ta'adda suka fara kai hari kan makarantu a Najeriya, lamarin da ya fara faruwa a shekarar 2014 a makarantar sakandaren ‘yan mata ta garin Chibok da ke jihar Borno a Arewa maso gabashin kasar. Bincike ya n…
  continue reading
 
A wannan mako, shirin ya yi duba ne a kan sabuwar hanyar koyarwa, da kuma tasirin da ta ke da shi a harkar ilimi a faɗin duniya, wato Innovative Teaching Method a turance. Ita dai sabuwar hanyar koyarwa wato Innovative Teaching Method, hanya ce da ta sha bambam da hanyoyin koyarwa da aka saba gani a lokutan baya, domin ita ana koyar da ɗalibai ne b…
  continue reading
 
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako, ya yi duba ne a kan tsarin ilimin kimiyya da fasaha tsantsa hadi da lissafi, wato STEM Education a turance. Mafi yawancin kasashen Duniya da suka ci gaba, na bawa wannan tsari na Ilimin Kimiyya da fasaha tsantsa hadi da Lissafi fifiko a makarantunsu, la’akhari da yadda kimiyya da fasaha a wannan zamani suk…
  continue reading
 
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako ya yi duba ne kan yadda ake ci gaba da samun ci gaba a bangaren daliban da ke zuwa makaranta a yankin Arewacin Najeriya. Jami'ar Umaru Musa 'Yar Adu'a da ke jihar Katsina ta samu nasarar yaye sama da dalibai dubu 10 a wannan shekarar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin ta re da Abdulkadir Ha…
  continue reading
 
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako ya duba yadda mallakar takardun kammala karatu na bogi a Najeriya ke barzana ga karewar kwararru a fannoni da dama. Ana fargabar idan har wannan dabi'a ta ci gaba a haka, tabbas za'a rasa kwararru musamman a fannin lafiya, kimiyya da sauransu. Danna Alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Shamsiyya H…
  continue reading
 
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan lokacin ya yi duba ne kan yadda wasu kungiyoyi karkashin cibiyar fasahar sadarwa da ci gaban al’umma wato CITAD suka samar da wata katafariyar cibiyar sadarwa da aka yiwa lakabi da HELLO HOPE a jahar Bauchi. Shirin ya kasance wani bangare na yunkurin saukakawa mazauna karkara hanyoyin samun sadarwa ta internet mu…
  continue reading
 
Matsalar tsaro na daya daga cikin matsalolin da ke addabar Najeriya, musamman ma arewacin kasar, hakan ya sanya sashen koyon aikin jarida na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria da ke jihar Kaduna ya shirya wani taro gagarumin taro na kasa da kasa domin tattaunawa a kan gudumawar da kafafen yada labarai za su iya bayarwa wajen warware matsalar tsaro. Y…
  continue reading
 
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan lokacin ya yi duba ne kan yadda dalibai da dama a Jamhuriyar Nijar, musaman maza ke barin karatu da sunan tafiya neman kudi, kasashen ketare kamar Libiya, Aljeriya ko kuma hako zinare a kasar Mali kai harma da kokarin tsallakawa Turai, abin da ya sanya kungiyoyin dalibai a kasar bazama aikin wayar da kan matasa k…
  continue reading
 
Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon zai yi duba ne kan yadda gwamnatin jahar Neja da ke Arewacin Najeriya, ta samar da shirin horas da dalibai sana'oin hannu don dogaro da kai. Gwamnatin jahar dai ta ware ranar Juma'ar kowane mako don gudanar da darasin koyon sana'oin hannu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsi…
  continue reading
 
A wannan makon zamu duba yadda ci gaban kimiyya da Ilimi ke zama wani nau’I na koma baya musamman a tsakanin dalibai a Najeriya. Tun bayan samar ko kuma kirkirar na’urar kwamfuta a 1837, da kuma shigowar ta Najeriya karon farko a 1963 sannu a hankali take bazuwa tsakanin jama’a, yayi da kuma ake samun ci gaba ta fannin amfani da ita.…
  continue reading
 
Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon zai yi duba ne da tsarin karatun 'yayan makiyaya, wato Nomadic Education. Gwamnatin jihar Neja ce ta yi hobbasa don farfado da shirin karatun 'yayan makiyaya a jihar. Shirin zai bai wa makiyaya damar samun ilimi a duk inda suka yi balaguro don inganta makomarsu. Yanzu haka dai shirye-shirye sun yyi nisa …
  continue reading
 
Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon tare da Shamsiyya Haruna ya maida hankali ne kan nazarin da masana kimiya suka yi wajen kirkirar Tabaraun hangen nesa, don taimakawa masu raunin gani. A jamhuriyar Nijar, matsalar gani na zama babban kalubale ga al'ummar kasar wacce a yanzu har aka fara samunta a tsakanin matasa. Tuni dai matsalar ta san…
  continue reading
 
Loading …

Quick Reference Guide