Yau public
[search 0]
More
Download the App!
show episodes
 
Artwork

1
Najeriya a Yau

Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim

Unsubscribe
Unsubscribe
Weekly+
 
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
  continue reading
 
Loading …
show series
 
Dawo da tsohon taken Najeriya da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi na shan yabo da suka. Mutane da dama dai na cewa a yanzu talakan Najeriya ba abin da yake bukata ba ke nan. Shirin Najeriya a Yau zai duba alfanun dawo da taken da muhimmancinsa a mizanin bukatun ’yan Najeriya.By Muslim Muhammad Yusuf
  continue reading
 
A yankuna da dama an fara samun ruwan sama, duk da cewa damina ba ta yi karfi ba a wasu wuraren. Bayanai sun nuna cewa a irin wannan lokaci Kwalara ko amai da gudawa da Maleriya da Thypoid da dai sauransu na cikin cututtukan da ke saurin yaduwa. Shirin Najeriya a Yau zai tattauna a kan wasu daga cikin waɗannan cututtuka da matakan kauce musu.…
  continue reading
 
Yau da Gobe shiri ne mai inganta rayuwar matasa cikin fadakarwa da ilmantarwa da kayatarwa, ya kuma karfafa mu su samun kaifin fahimtar matsalolin da suka addabe su, suka dabaibaiye su a wannan zamani. Shirin Yau da Gobe na zuwa sau biyar a mako, Litinin zuwa Jumma’a, daga karfe 4 da rabi na yamma zuwa karfe 5!Yau da Gobe ya hada komai, daga filin …
  continue reading
 
A ‘yan shekarun da suka gabata tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya sanya hannu a kan wata doka da ta karkasa Masarautar Kano gida biyar, daga bisani kuma ya tsige sarkin Kano na 14 bisa zargin aikata ba daidai ba da rashin da’a. Yanzu kuma gashi shekaru hudu bayan hakan, gwamnan Kano na yanzu Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka…
  continue reading
 
Batun cire sarakun da aka faro ta kamar wasa ga shi ta tabbata. Sarki Sanusi shi ne sarkin da ya sake dawowa bayan tube sarakuna biyar na jihar, lamarin da za a iya cewa wasu sun yi hasashen hakan tun da fari. Shin mene ne mataki na gaba da ya rage wa sarakunan? Ya alaka za ta kasance tsakanin wadanna gidajen sarautar. Shirin Najeriya a Yau ya tatt…
  continue reading
 
Alkiblar siyasa da ke kaɗawa daga ɓangaren ‘yan adawa ta fara daukar hankalin jam’iya mai mulki. Yawaitar ganawar da aka hangi wasu jiga-jigan adawa na yi ta sa ana diga ayar tambaya me ke shirin faruwa, lamarin da jam’iyar APC ta ce 'yan Najeriya za su bude idanunsu kada su yarda da irin mutanen da tace suna kasuwar bukata. Toh shin wannan ganawa …
  continue reading
 
Wata kalma da ’yan Najeriya ke yawan ji ita ce ƙimar hauhawar farashi, wato ‘Inflation rate’ a turance. Sai dai kuma ba kowa ne ya fahimci abin da Kalmar take nufi ba, balle ya san yadda ake auna hauhawar farashin. Shin ta yaya yan kasa za su gane tasirin hakan a rayuwarsu ta yau da kullum? Shirin Najeriya a Yau zai yi kokarin amsa muku wadaannan t…
  continue reading
 
Yau da Gobe shiri ne mai inganta rayuwar matasa cikin fadakarwa da ilmantarwa da kayatarwa, ya kuma karfafa mu su samun kaifin fahimtar matsalolin da suka addabe su, suka dabaibaiye su a wannan zamani. Shirin Yau da Gobe na zuwa sau biyar a mako, Litinin zuwa Jumma’a, daga karfe 4 da rabi na yamma zuwa karfe 5!Yau da Gobe ya hada komai, daga filin …
  continue reading
 
Shin kun taba cin karo da yara masu jijjiga? wani yanayi ne da larurar kwakwalwa ko kasancewar guba a cikin jinni kan haifar wa manya, zazzabi mai tsanani kuma kan haifar wa yara. Yanayin kan sa yaro ya shiga yanayin sarkewar gabobin jiki da numfashi kamar dai mai farfadiya a wasu lokutan. Shirin Najeriya a Yau na dauke labarin wata matar da irin h…
  continue reading
 
A wannan zamani da mutum zai iya samun bashi kaitsaye ta waya daga manhajoji daban-daban amma idan mutum ya kasa biya kamfanonin bada bashin kan aika sakonnin cin zarafi da barazana har ga ‘yan uwan wanda ya ci. Duk da gargadin da hukumomi mutane da dama na kukan ana ɓata musu suna, kuma an kasa kulle irin wadannan manhajoji kamar yadda aka ce. Shi…
  continue reading
 
Gwamnatin tarayyar ta ce za a ɓullo da tsarin auna ƙwazon ma’aikata bisa mizani ta yadda dagewar ma’aikaci zai sa ya samu ƙarin girma ko albashin ma zai iya bambanta, wato dai iya kwazonka iya albashinka. Irin wannan yunkuri na gwamnatin tuni ma’aikata da ‘yan kwadago suka fara suka da tunanin wata manufa ce ta kauda hankali. Toh ko ta fannin shari…
  continue reading
 
A baya-bayan nan mazauna manyan biranen Najeriya na ta kokawa game da yadda masu gidajen haya ke neman mai da su saniyar tatsa wajen tsuga kudin haya. Sai dai masu gidajen na cewa ana fama da tsadar rayuwa kuma kula da irin wadannan gidaje na cin kudi sosai. Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari kan yadda lamarin ke shafar rayuwar mutanen da suke zaun…
  continue reading
 
Yau da Gobe shiri ne mai inganta rayuwar matasa cikin fadakarwa da ilmantarwa da kayatarwa, ya kuma karfafa mu su samun kaifin fahimtar matsalolin da suka addabe su, suka dabaibaiye su a wannan zamani. Shirin Yau da Gobe na zuwa sau biyar a mako, Litinin zuwa Jumma’a, daga karfe 4 da rabi na yamma zuwa karfe 5!Yau da Gobe ya hada komai, daga filin …
  continue reading
 
Takaddama a tsakanin gwamantin Tarayya da ta jihar Zamfara a kan hanyar da ya kamata a bi don kawo karshen matsalar tsaro na neman yin kafar ungulu ga yunkurin kawar da barazanar ’yan bindiga. Gwamnatin Jihar ta Zamfara dai ta sa kafa ta shure duk wani yunkuri na sasantawa da ‘yan bindiga tana mai cewa ba da ita ba, sannan ta zargi gwamnatin Tarayy…
  continue reading
 
Ga alama nan ba da dadewa ba yanayin sana’ar POS a kasar nan zai sauya. Babban Bankin Najeriya (CBN) ya wajabta wa masu wannan sana’a yin rajista da Hukumar Rajistar Kamfanoni da Kungiyoyi (CAC) zuwa nan da 7 ga watan Yulin 2024. To amma ya batun harajin da suke korafi a kai? Ku biyo mu a Shirin Najeriya a Yau don jin matsayar CAC game da biyan kud…
  continue reading
 
Sabuwar dokar da gwamnatin jihar Kano ta sanyawa hannu kan yin gwajin lafiya kafin aure na shan yabo da suka. A cewar gwamnatin, yawaitar yaduwar cututuka a tsakanin ma’aurata bayan aure shi ne makasudin yin wannan doka. Amma me ya sa za a daure wanda ya taka dokar tsawon shekara 5 ko tarar 500,000? Idan aka samu wanda ya taka dokar miji za a daure…
  continue reading
 
Loading …

Quick Reference Guide