Jari public
[search 0]
More
Download the App!
show episodes
 
Artwork

1
Sunday Monday Podcast

Rini, Satria, and Rori

Unsubscribe
Unsubscribe
Monthly
 
Terjun bebas ke pembahasan drama kehidupan dari sudut pandang tiga host dengan kepribadian berbeda. Simak petualangan mereka dalam bentuk obrolan panjang, mentah, dan uncensored di Sunday Monday Podcast! Pick your casters! 🌟Rini: INTP-Taurus-True Neutral Tenaga kreatif absurdis nan ceria yang kerap bergumul dengan krisis eksistensial. 🌟Satria: INFJ-Scorpio-Lawful Evil Fotografer konser penyuka romansa yang lebih senang di rumah saja. 🌟Rori: ENFJ-Aries-Chaotic Good Gitaris kece yang bisa dipa ...
  continue reading
 
Artwork

1
Najeriya a Yau

Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Unsubscribe
Unsubscribe
Weekly+
 
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
  continue reading
 
Luangkan minit-minit keemasan anda bersama Dr. Hj. Tengku Asmadi dalam Mutiara Minda. Beberapa minit setiap hari mampu merubah mindset dan cara fikir anda. Apabila mindset berubah, maka berubahlah sikap dan tingkah laku. Berubahlah juga tindakan dan aksi anda dan ini membawa hasil baru, atau pencapaian baru dalam hidup anda.
  continue reading
 
Loading …
show series
 
Send us a Text Message. Masana na nuna fargaba game da rashin tabbas a harkar zuba jari a Najeriya. Tun a watannin da suka gabata ake ta samun ficewar manyan kamfanoni daga kasar, lamarin da ake alakantawa da wasu tsare-tsaren tattalin arziki. Shirin Najeriya a yau zai tattauna kan yadda hakan zai ci gaba da tasiri a kan tattalin arzikin Najeriya.…
  continue reading
 
Send us a Text Message. Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta soke dokar da ta kirkiri hukumomin raya wasu biranen jihar uku. Wannan mataki dai ya haifar da zazzafar muhawarar a kan nasabarsa da nuna yatsa da ake yi a tsakanin gwamnati mai ci da wadda ta gada. Shirin Najeriya a Yau zai binciki dalilin daukar wannan mataki da yadda zai shafi ci gaban ka…
  continue reading
 
Send us a Text Message. A lokuta da dama idan ran ‘yan kasa ya baci su kan dauki matakin nuna fushinsu ga gwamnati ta hanyar zanga-zanga. Ana yawan kokwantn shin zanga-zangar da ake gudanarwa a Najeriya suna haifar da ɗa mai ido? Ta wace hanya zanga-zanga ta zama silar samar da maslaha? Ku biyo mu cikin Shirin Najeriya a yau.…
  continue reading
 
Send us a Text Message. Jihohin Zamfara da Neja a Arewacin Najeriya na cikin jihohin da ke fuskantar kalubalen tsaro duk da tarin ma’adanai da suke da su. Sai dai duk da zafin hare-haren da ake samu a wadannan jihohi aikin hakar ma’adanai na ci gaba kamar yadda aka saba. Shin wace alaka ke tsakanin masu hakar ma’adanai da ‘yan bindiga? Wani bincike…
  continue reading
 
Send us a Text Message. Ana musayar yawu kan ’yancin ’yan kasa na fadin albarkacin bakinsu game da manufofin gwamnati mai ci. ’Yan adawa na zargin jam’iyar APC mai mulki da kokarin rufe bakin masu yi mata gyara a inda ta yi kuskure. Shirin Najeriya a yau zai tattauna ne a kan abin da ya sa hakan yake faruwa.…
  continue reading
 
Send us a Text Message. Gwamnoni da dama a Najeriya sun bayyana aniyarsu ta gudanar da zabukan kananan hukumomi kafin karshen wannan shekarar. Zuwa yanzu jihohi 13 aka lissafa za su gudanar da zabubbukan, lamarin da wasu ke alakantawa da hukuncin Kotun Koli da ya bai wa kananan hukumomin ’yancin cin gashin kai. Shirin Najeriya a yau zai yi bincike …
  continue reading
 
Send us a Text Message. A yau ne ake kammala azumin Tasu'a da Ashura, wato na kwanakin Tara da Goma cikin watan farko na kalandar Musulunci da Musulmai ke yi. Azumi ne da ake yi cikin watan Muharram, wanda malamai ke cewa yana daya daga cikin watanni hudu mafiya Alfarma a shekarar Musulunci. Shirin Najeriya a Yau ya duba yadda ake azumin Tasu'a da …
  continue reading
 
Send us a Text Message. Hukuncin kotun koli kan ikon kananan hukumomi ya jefa su cikin farin ciki a fadin Najeriya. Sai dai yanzu abin da ake son ganin ya faru shi ne yaushe wannan tsari zai yi tasiri kuma me ya rage ga kananan hukumomi. Shirin Najeriya a Yau ya yi fashin bakin kan abin da hukuncin ya kunsa da mataki na gaba ga kanana hukumomi.…
  continue reading
 
Send us a Text Message. A wannan makon babban malamin Addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman ya samu ni’imar cika shekara 100 a duniya. Malamai da mabiya da al’umma sun jinjina yadda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidima ga Addini. Shirin Najeriya a Yau zai yi nazari a kan gudummuwar da Shehin Malamin ya bayar a cikin shekara fiye da 70 da ya yi yan…
  continue reading
 
Send us a Text Message. Labarin bullar wata kungiyar da ake zargin tana rajin yada akidar auren jinsi a Kano na ci gaba da yamusta hazo. Tuni hukumomi suka bayyana matakin da za su dauka a kan wadannan zarge-zarge duk da yake sun amince cewa sun taba ganawa da kungiyar. Shirin Najeriya a Yau zai bincika yadda aka yi ana zaton wuta a makera, ta tash…
  continue reading
 
Send us a Text Message. Jihohi da dama a wannan lokaci sun fada cikin yanayin dogayen layukan mai da kuma karancinsa. Wasu gidajen mai sun kasance a kulle yayin da masu siyarwar kuma farashin sai wanda ya gani, baya ga ‘yan bumburutu da ke cin kasuwarsu a bayan fage. Shirin Najeriya a Yau domin jin dalilin wahalar mai a Najeriya…
  continue reading
 
Send us a Text Message. Zuwa yanzu masu shan wutar lantarki da ke tsarin Band A sun samu sanarwar kara kudin wutar lantarki Sai dai wasu na ganin ba a iya biyan bukatun da wannan kari ba zai samu muhalli ba Shirin Najeriya a Yau zai tattauna ne kan Dalilin da ya sa ake kara wa masu tsarin Band A kudin lantarki a kai a kai.…
  continue reading
 
Send us a Text Message. Ana ta musayar ra’ayin bayan da Kamfanin man fetur na kasa NNPCL ya ayyana dokar ta-ɓaci kan harkokin haƙowa da kuma fitar da ɗanyen mai daga ƙasar. Mutane na neman amsar shin me hakan ke nufi, da muhawarar ko hakan abu mai yiwuwa ne? Shirin Najeriya a Yau nzai tattauna kan abin da dokar ta baci kan man fetur ke nufi.…
  continue reading
 
Send us a Text Message. Ana ci gaba da samun koke-koke game da yadda ‘yan kasa ke ji a jikinsu. Masana dai na ganin akwai matakan da in har gwamnati ta dauke su za a iya kawar da matsin tattalin arzikin da ta yi wa talaka dabaibayi. Shirin Najeriya a Yau zai tattauna kan matakan gaggawa da suka kamata gwamnati ta dauka domin kaiwa share hawayen ‘ya…
  continue reading
 
Send us a Text Message. Masu fafutukar kare muhalli suna cewa yadda ’yan Najeriya suke shakulatin bangaro da tsaftar muhalli abin damuwa ne. Yayin da ake bikin Ranar Kula Da Tsaftar Muhalli Ta Kasa a yau, shirin Najeriya a Yau zai tattauna a kan halin da Najeriya ke ciki da abin da hukumomi suke yi game da tsaftar muhalli.…
  continue reading
 
Send us a Text Message. A baya-bayan nan ana samun muhawara, wani lokaci ma zazzafa, a kan kimar masarautun gargajiya. Shin yaya al’umma ke kallon sarakunan gargajiya a halin yanzu? Shirin Najeriya a Yau zai tattauna a kan kimar masu rike da masautun gargajiya a wannan zamani.By Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim da Sulaiman Hassan
  continue reading
 
Send us a Text Message. Gwamnonin Arewa maso yamma suna wani babban a taron tsaro da nufin lalubo hanyar kawar da matsalar tsaro a yankin. Hukumar Raya Kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya ce ta shirya taron da hadin gwiwar Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma domin hada kan gwamnatocin yankin. Shin ta wace hanya gwamnonin za su iya cimma wannan buri?…
  continue reading
 
Send us a Text Message. Masu bibiyar tirka-tirkar masarautun Kano na ci gaba da shiga ruɗani bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya. Ko wane bangare na murnar shi ne yake da nasara, lamarin da ya sa mutane tambayar shin wane ne Sarki? Don fahimtar inda wannan hukuncin ya dosa, ku biyo mu cikin shirin Najeriya a Yau.…
  continue reading
 
Send us a Text Message. Wasu kalaman da jagoran Kwankwasiyya Rabi’u Musa Kwankwaso ya furta yana zargin Gwamnatin Tarayya suna ci gaba da tayar da kura. Fadar shugaban kasa da jam’iyyar APC a matakin kasa da jihar Kano sun yi kakkausan suka da kiran a yi maza-maza a kama shi. Shin me ya girgiza Jam’iyyar ta APC game da wadannan kalamai? Shirin Naje…
  continue reading
 
Send us a Text Message. A kullum farashin kayan abinci kara tashi yake yi a Najeriya. Masu sharhi kuma suna ta kokarin bayar da shawarwari a kan hanyoyin fita daga wannan yanayi. Shirin Najeriya a Yau zai tattauna kan wadannan hanyoyi da tasirin da za su iya yi.By Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim, Sulaiman Hassan
  continue reading
 
Send us a Text Message. A lokacin Bikin Babbar Sallah da mutane kan yi layya, ana sa ran wanda bai yi ba ma ya samu ya ci nama. Amma wasu masu karamin karfi kan bayyana yadda makwabtansu da suka yi layya sukan shige da namansu gida su yi tuwo-na-mai-na. Shirin Najeriya a Yau zai duba halalcin yin hakan a Musulunce.…
  continue reading
 
Send us a Text Message. Gwamnatocin Kananan Hukumomi sun koka cewa za a dora musu nauyi idan har aka amince da N62,000 a matsayin mafi karancin albashi. Sai dai ma’aikatansu na ganin ba su dalilin fadin hakan, ganin yadda suka samu ninkin kudaden shiga bayan cire tallafin man fetur. Ku biyo mu cikin Shirin Najeriya a Yau domin jin yadda za a warwar…
  continue reading
 
Send us a Text Message. Gurbacewar iska na ci gaba da jan hankalin masu ruwa da tsaki a duniya. Hukumomi sun ce ‘yan Najeriya na amfani da wasu abubuwa da ke bayar da gudummuwa wajen gurbacewar iskar da muke shaka da barazana ga lafiyar dan adam. Shin ya girmar matsalar take a Najeriya? Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan wannan batu.…
  continue reading
 
Send us a Text Message. Kiraye-kiraye na karuwa game da matakin da ya kamata a dauka don dakile matsalar karancin abinci mai gina jiki wato tamowa a jikin kanan yara Kungiyar likitoci ta 'Doctors Without Borders' ta ce an samu ƙaruwar yara masu fama da tamowa a jihohi 11 da ke arewacin Najeriya. Shirin Najeriya a Yau zai duba matakan da za ya kamat…
  continue reading
 
Send us a Text Message. A yayin da damina ta fara kankama a wasu sassan Najeriya, fatan manoma shi ne samun yabanya mai kyau. Akwai matakan da masana ke ganin ya kamata manoma su dauka duk a lokacin da ruwa ya fara sauka domin kauce wa lalacewar amfanin gona. Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan matakan da suka kamata manoma za su dauka a wannan y…
  continue reading
 
Send us a Text Message. Yayin da muhawara ta yi zafi a kan mafi ƙarancin albashi, inda kungiyoyin kwadago ke bukatar a biya Naira 494,000, wasu kamfanoni da gwamnati kuma suke ganin a yi karin da hankali zai dauka, me ma’aikata da kansu suke ganin ya fi dacewa? Shirin Najeriya a Yau zai duba wannan domin an ce mai daki shi ya san inda yake yi mishi…
  continue reading
 
Send us a Text Message. Bangaren shari’a yana cikin ginshikai uku na mulkin dimokradiyya. A cikin shekara 25 da aka yi ana mulkin dimokradiyya ba tare da katsewa ba wannan bangare ya fuskanci kalubale da dama. Shirin Najeriya a Yau ya yi duba a kan wannan lamari.By Muslim Muhammad Yusuf da Sulaiman Ibrahim
  continue reading
 
Send us a Text Message. Dawo da tsohon taken Najeriya da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi na shan yabo da suka. Mutane da dama dai na cewa a yanzu talakan Najeriya ba abin da yake bukata ba ke nan. Shirin Najeriya a Yau zai duba alfanun dawo da taken da muhimmancinsa a mizanin bukatun ’yan Najeriya.…
  continue reading
 
Send us a Text Message. A yankuna da dama an fara samun ruwan sama, duk da cewa damina ba ta yi karfi ba a wasu wuraren. Bayanai sun nuna cewa a irin wannan lokaci Kwalara ko amai da gudawa da Maleriya da Thypoid da dai sauransu na cikin cututtukan da ke saurin yaduwa. Shirin Najeriya a Yau zai tattauna a kan wasu daga cikin waɗannan cututtuka da m…
  continue reading
 
Send us a Text Message. A ‘yan shekarun da suka gabata tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya sanya hannu a kan wata doka da ta karkasa Masarautar Kano gida biyar, daga bisani kuma ya tsige sarkin Kano na 14 bisa zargin aikata ba daidai ba da rashin da’a. Yanzu kuma gashi shekaru hudu bayan hakan, gwamnan Kano na yanzu Abba Kabir Yusuf ya s…
  continue reading
 
Send us a Text Message. Batun cire sarakun da aka faro ta kamar wasa ga shi ta tabbata. Sarki Sanusi shi ne sarkin da ya sake dawowa bayan tube sarakuna biyar na jihar, lamarin da za a iya cewa wasu sun yi hasashen hakan tun da fari. Shin mene ne mataki na gaba da ya rage wa sarakunan? Ya alaka za ta kasance tsakanin wadanna gidajen sarautar. Shiri…
  continue reading
 
Send us a Text Message. Alkiblar siyasa da ke kaɗawa daga ɓangaren ‘yan adawa ta fara daukar hankalin jam’iya mai mulki. Yawaitar ganawar da aka hangi wasu jiga-jigan adawa na yi ta sa ana diga ayar tambaya me ke shirin faruwa, lamarin da jam’iyar APC ta ce 'yan Najeriya za su bude idanunsu kada su yarda da irin mutanen da tace suna kasuwar bukata.…
  continue reading
 
Send us a Text Message. Wata kalma da ’yan Najeriya ke yawan ji ita ce ƙimar hauhawar farashi, wato ‘Inflation rate’ a turance. Sai dai kuma ba kowa ne ya fahimci abin da Kalmar take nufi ba, balle ya san yadda ake auna hauhawar farashin. Shin ta yaya yan kasa za su gane tasirin hakan a rayuwarsu ta yau da kullum? Shirin Najeriya a Yau zai yi kokar…
  continue reading
 
Send us a Text Message. Shin kun taba cin karo da yara masu jijjiga? wani yanayi ne da larurar kwakwalwa ko kasancewar guba a cikin jinni kan haifar wa manya, zazzabi mai tsanani kuma kan haifar wa yara. Yanayin kan sa yaro ya shiga yanayin sarkewar gabobin jiki da numfashi kamar dai mai farfadiya a wasu lokutan. Shirin Najeriya a Yau na dauke laba…
  continue reading
 
Send us a Text Message. A wannan zamani da mutum zai iya samun bashi kaitsaye ta waya daga manhajoji daban-daban amma idan mutum ya kasa biya kamfanonin bada bashin kan aika sakonnin cin zarafi da barazana har ga ‘yan uwan wanda ya ci. Duk da gargadin da hukumomi mutane da dama na kukan ana ɓata musu suna, kuma an kasa kulle irin wadannan manhajoji…
  continue reading
 
Send us a Text Message. Gwamnatin tarayyar ta ce za a ɓullo da tsarin auna ƙwazon ma’aikata bisa mizani ta yadda dagewar ma’aikaci zai sa ya samu ƙarin girma ko albashin ma zai iya bambanta, wato dai iya kwazonka iya albashinka. Irin wannan yunkuri na gwamnatin tuni ma’aikata da ‘yan kwadago suka fara suka da tunanin wata manufa ce ta kauda hankali…
  continue reading
 
Send us a Text Message. A baya-bayan nan mazauna manyan biranen Najeriya na ta kokawa game da yadda masu gidajen haya ke neman mai da su saniyar tatsa wajen tsuga kudin haya. Sai dai masu gidajen na cewa ana fama da tsadar rayuwa kuma kula da irin wadannan gidaje na cin kudi sosai. Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari kan yadda lamarin ke shafar rayu…
  continue reading
 
Send us a Text Message. Takaddama a tsakanin gwamantin Tarayya da ta jihar Zamfara a kan hanyar da ya kamata a bi don kawo karshen matsalar tsaro na neman yin kafar ungulu ga yunkurin kawar da barazanar ’yan bindiga. Gwamnatin Jihar ta Zamfara dai ta sa kafa ta shure duk wani yunkuri na sasantawa da ‘yan bindiga tana mai cewa ba da ita ba, sannan t…
  continue reading
 
Send us a Text Message. Ga alama nan ba da dadewa ba yanayin sana’ar POS a kasar nan zai sauya. Babban Bankin Najeriya (CBN) ya wajabta wa masu wannan sana’a yin rajista da Hukumar Rajistar Kamfanoni da Kungiyoyi (CAC) zuwa nan da 7 ga watan Yulin 2024. To amma ya batun harajin da suke korafi a kai? Ku biyo mu a Shirin Najeriya a Yau don jin matsay…
  continue reading
 
Send us a Text Message. Sabuwar dokar da gwamnatin jihar Kano ta sanyawa hannu kan yin gwajin lafiya kafin aure na shan yabo da suka. A cewar gwamnatin, yawaitar yaduwar cututuka a tsakanin ma’aurata bayan aure shi ne makasudin yin wannan doka. Amma me ya sa za a daure wanda ya taka dokar tsawon shekara 5 ko tarar 500,000? Idan aka samu wanda ya ta…
  continue reading
 
Send us a Text Message. Yanayin da ake ciki na tsadar rayuwa ne ya sa kowa ya koma neman kudi da mota don daukar fasinjan a Abuja. Sai dai hukumomi sun ce an dauki matakin hana duk wani mutum da bai cika ka'idojin yin tasi ba. Shirin Najeriya a Yau ya duba dalilan da suka sa hukumomi ke shirin tabbatar da halascin yin kabu-kabun ga masu zaman kansu…
  continue reading
 
Send us a Text Message. A karshen shekarar 2023 ne dai, hukumar Lafiya ta Duniya WHO da Cibiyar hana yaduwar cututtuka suka yi gargadi cewa cutar kyanda na ci gaba da zama barazana ga yara a Najeriya. Sai ga shi kwatsam an samu rahotanni game da barkewar cutar a wasu yankunan Naijeriya har ta kashe wasu mutane da dama. Shirin Najeriya a Yau ya maya…
  continue reading
 
Send us a Text Message. Masu amfani da shafukan sada zumunta kan fada hannun masu dandantsa inda sukan yi kutse a shafin mutum har ya rasa iko da shi. Kwararru sun ce ana yi wa wasu hakan domin bata suna ko kuma neman kudi da damfara. Shirin Najeriya a Yau ya tattauna da kwararru a fannin samar da matakan tsaro a soshiyal midiya game da dabarun ing…
  continue reading
 
Send us a Text Message. Shafukan sada zumunta na ta girgiza bayan da wani labari ya bayyana game da yanayin walwalar ma’aikata da albashinsu a jihar Borno. Ma’aikata da dama sun yi ta yada hoton albashinsu na N7,000; wasu N8,000 ko N13,000 ko N15,000 ga ma’aikatan lafiya. Shirin Najeriya a Yau ya gano gaskiyar abin da ya sa gwamnatin jihar Borno ke…
  continue reading
 
Loading …

Quick Reference Guide