Kukan Zuci shiri ne wanda aka sadaukar da shi don wayar da kan al'umma game da halin rayuwa da mata ke tsintar kansu a ciki. Shiri ne da jaridar WikkiTimes za ta rinƙa kawo muku duk bayan sati biyu. Kukan Zuci zai bada gudumawa ta hanyar ba da dandali ga mata don bayar da labarin rayuwar su. Wannan shiri zai maida hankali kan wahalhalun da ake sha a cikin auratayya da kuma nuna wariya da kyamar ga yara mata cikin al’umma yayin da suka samu kansu cikin kalubalen rayuwa.
…
continue reading
Kukan Zuci: Zainab's StoryBy WikkiTimes
…
continue reading
Wannan faifai zai bada labarin Zainab, wacce tayi fice a harkar aikin jarida wanda ya kasance burinta tun tana ƙarama. Sai dai kash, wasu ƙalubale suna barazana ga wannan aikin nata tare da gusar da soyayyar da take yi wa aikin. Shin wasu ƙalubale Zainab ke fuskanta? Ku biyo mu.By Hafsat Muhammad
…
continue reading
A wannan faifayi, zamu bayyana labarin Sadia wacce tayi dana sanin aurenta da Salihu, sakamakon sikila da suka haifa da kuma rasa gurbin karatu data yi.By Hafsat Muhammad
…
continue reading