RFI Hausa public
[search 0]
Download the App!
show episodes
 
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.
  continue reading
 
Artwork
 
Shirin yakan duba yadda kasuwanci da tattalin arizikin kasashen duniya ke ciki. Kana yakan ji sabbin dubaru da hanyoyin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masana’antu dangane da halin da suke ciki.
  continue reading
 
Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.
  continue reading
 
Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Jumma'a da safe.
  continue reading
 
Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-daban na duniya, tare da nazari kan irin ci gaban da aka samu wajen binciken kimiya da fasaha da ke neman saukakawa Dan’adam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Bil’adama. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe, a ku maimata ranar Alhamis.
  continue reading
 
Fili ne na musamman kan Fina-finai ta hanyar tattauna da masu ruwa da tsaki a wannan fanni a duniya, Tare da wayar wa ma su sauraro kai da kara masu basira dangane da hikimar da Allah ya bai wa wasu ta fanin shirya fim ko tsara wasan kwaikwayo. Wanda ke zo maku a duk ranar Asabar da safe, tare da maimaici a ranar Lahadi da yamma.
  continue reading
 
Shirin Dandalin Siyasa, yana tattaunawa tare da tafka muhawar kan al’amurran siyasa da ke faruwa a kasashen duniya, da batutuwan da suka shafi al’umma kai tsaye, wanda Bashir Ibrahim Idris ke jagoranta. Wannan Shirin na zuwa ne a karshen mako Ranar Assabar da maimaci a ranar Lahadi a Shirye Shiryen Safe da Yamma.
  continue reading
 
Shirin Al’adu, kida da fina-finai, shiri ne da ke zo maku a ranakun assabar da kafe 5:30 na yamma, tare da maimaici da karfe 8:00 na safiyar ranar Lahadi.Inda muke kawo ma ku rahotanni da labaran da suka shafi Fina-finai na gida da ketare, firarraki da mawakammu na gargajiya da na zamani, tare da kawo maku labaran da suka shafi al’adummu na gida da ketare. Tare da naku Mahaman Salisu Hamisu.
  continue reading
 
Loading …
show series
 
A yau shirin zai waiwai kasar Ghana, inda basusukan da ake bin kasar ya karu da dala biliyan 47.4 / Cidi biliyan 658.6 a cikin watanni biyun farko na shekarar 2024. Babban Bankin ƙasar ta Ghana ne ya fitar da wadandan alkaluma cikin wani rahoton da ya fitar na taƙaitaccen Bayanan Tattalin Arziki da Kuɗi na watan Mayun shekarar 2024. A cewar babban …
  continue reading
 
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci al’ummar ƙasar su jingine zanga-zanga tare da bayyana aniyar tattaunawa don laluɓo masalaha. A jawabin da ya gabatar sakamakon zanga-zangar tsadar rayuwa da ta ɓarke a akasarin sassan ƙasar, Tinubu ya shaida wa ƴan Najeriya cewa yana jin raɗaɗin da suke ji, kuma tabbas zai samo mafita. Yaya wannan jawab…
  continue reading
 
Wasannin guje-guje da tsalle-tsalle da ke gudana a nan birnin Paris na tafiya yadda aka tsara, inda kawo yanzu an kammala wasu wasanni da dama wasu kuma ana daf da kammala su. 'Yan wasan tawagar kwallon kwando ta Mata ta Najeriya na ci gaba da fatan ganin a wannan karon ta samu nasarar tsallake matakin rukuni, ganin yadda suka dage wajen lashe wasa…
  continue reading
 
Mu Zagaya Duniya, shiri ne da ya saba tacewa gami da zaɓo wasu daga cikin muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya ƙare domin bitarsu tare da Nura Ado Suleiman. Shirin wannan makon ya fi mayar da hankali ne wajen bitar yadda zanga-zanga kan tsadar rayuwa da kuma neman shugabanci nagari ta gudana a sassan Najeriya, inda a wasu sassa za…
  continue reading
 
Shirin ra'ayoyin ku masu saurare na wannan rana ya duba yadda rashin tsrao da kuma garkuwa da mutane ke kara yawaita a arewacin Najeriya, inda a baya-bayan nan kwamishin yan sandan jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya ya sanar da cafke 'dan majalisar dokoki da hakimi tare da tsohon shugaban karamar hukumar Kaurar Namoda bisa zarginsu da hannu dumu…
  continue reading
 
A wannan mako, shirin ya yi duba ne a kan tsarin dabarun koyo da koyarwa a ƙarni na 21 da ake kira da 21st Century Learning Skills a turance.Tsarin dabarun koyo da koyarwa na ƙarni na 21, an soma amfani da shi tun a shekarar 2001 domin zamanantar da tsarin yadda ake koyarwa ta hanyar samar da dabarun zamani da za su taimaka wa malamai wurin fahimta…
  continue reading
 
Shirin ra'ayoyin masu saurare na wannan rana ya mayar da hankali ne kan yadda kungiyoyin mayaka masu ikirarin jihadi ke kara zafafa hare-hare a kasashen yankin Sahel. Hare-haren mayakan ya fara tsallakawa zuwa kasashen Jamhuriyar Benin da Togo wadanda basu saba ganin irin haka a kasashen su ba. Ina ne kuke ganin ya kamata mahukunta su kara azama do…
  continue reading
 
A wannan mako shirin ya mayar da hankali ne kan wani rahoto da hukumar ƙididigar ta Najeriya ta fitar cewa an sake samun hauhawan farashin kayayyaki wanda ƙasar ba ta taɓa gani ba cikin shekaru 30, daidai lokacin da gwamnatin ƙasar ke faɗi tashin kawowa al’umma sauƙi kan tsananin rayuwa da suke ciki, tare da amincewa da Naira dubu 70 a amatsayin ma…
  continue reading
 
Taƙaddamar da ta kunno kai tsakanin hamshaƙin attajirin nahiyar Afirka Aliko Dangote da kamfanin man Najeriya NNPCL na ƙara yin ƙarfi a ‘yan kwanakin baya bayan nan, bayan da yayi korafin da ya yi cewar ana yiwa matatarsa zagon kasa, yayin da kamfanin ya mayar da martanin cewar Dangote bashi da lasisi, kuma yana son gwamnati ta soke lasisin masu sh…
  continue reading
 
Shirin na wannan mako zai yi duba ne kan Kabilar Gwari da ake samun su a tsakiyar Najeriya. Kabilar Gwari da bahaushe ke kira da "Gwarawa" na da al'adu daban-daban masu ban mamaki da suka sha banban da sauran kabilun mutanen da ke kewaye da su. Domin jin cikakken shirin dannan alamar saurare tare da Abdullahi Isa…
  continue reading
 
Shirin na wannan mako ya mayar da hankali ne kan karuwar matasan da basa zuwa makaranta a Ghana. Hukumar kididdiga ta kasar GSS ta gano cewa kusan matasa miliyan biyu ne ba sa karatun Boko ko aikin yi ko kuma samun horon sana'o'in dogaro da kai. Ku danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abdulkadeer Haladu Kiyawa.…
  continue reading
 
Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon zai mayar da hankalli ne a kan gargaɗin da hukumar kiyaye ingancin abinci da magunguna a Najeriya, wato NAFDAC ta yi a kan hatsarin da ke tattare da amfani da maganin kashe ƙwari na Sniper a wajen adana kayan abinci domin kare su daga ƙwari. NAFDACdai ta jaddada haramcin da ta yi a kan amfani da wannan magani…
  continue reading
 
Yau shirin zai yi, duba ne kan yaddata kaya a game da sshirye-shiryen gudanar da gasar olympics da za a fara a cikin wannan watann a birnin Paris. shirye-shirye dai sun yi nisa a game da wannan gasa, duba da cewa ilahirin tawagogin kasashe sama da ɗari 2 da za su fafata a wasanni dabam-dabam sun sauka a wannan birni, haka ma mabobin kwamitin shirya…
  continue reading
 
Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka’ na wannan mako zai yi dubi ne kan shirin gwamnatin Najeriya na ɓullo da tsarin biyan haraji kan masu gurbata muhalli ta wajen ayyukan da suke gudanarwa, wanda a turance ake kira carbon tax. Kuma ana sa ran wannan harajin zai tursasa wa masana’antu da ke gurbata muhalli yin takatsantsan. Wannan sabon haraji dai har yanz…
  continue reading
 
A ranar Alhamis da ta gabata, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da naira dubu 70 a matsayin mafi ƙarancin albashi a ƙasar, inda yayi alƙawarin sake nazari kan yiwuwar wani ƙarin a duk bayan shekaru uku, a cikin shirin mu Zagaya Duniya ,Nura Ado Suleiman ya zaɓo wasu daga cikin muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya ƙare …
  continue reading
 
Wakilan ƙasashe 28 sun gana da mahukuntan Libya kan hanyar da za su bi wajen dakile matsalar kwararar dubban bakin hauren da ke tsallaka Teku don shiga nahiyar Turai. A shekarun baya bayan nan Libya ta zama babbar cibiyar da ‘yan ci rani daga Afrika ke bi wajen tsallaka teku zuwa Turai, inda alkaluma suka nuna cewar, daga farkon wannan shekara zuwa…
  continue reading
 
Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' a wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan sabon matakin gwamnatin Najeriya na sahale shigo da muhimman kayan abinci kamar su shinkafa da wake da alkama da masara ba tare da biyan ƙudin fito ba har tsawon watanni 5, domin rage tasirin tsaɗar kayan abinci da ƴan ƙasar ke fama da shi tun bayan ɗarewar …
  continue reading
 
A wannan mako, shirin ya mayar da hankali ne kan yadda tsadar kuɗin wutar lantarki ke gurgunta harkokin karatu a manyan makarantun Najeriya. Kamar yadda aka sani, harkokin gudanarwar yau da kullum na manyan makarantu ba za su taɓa yiwu wa yadda ya kamata ba, muddin babu ingantacciyar wutar lantarki. To sai dai, baya ga rashin tsayayyiyar wutar a ku…
  continue reading
 
Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya tattauna ne kan tasarin nau'ukan abinci da akan ƙirkira a ɗakunan bincike wadanda ake kira Synthetic foods a turance, domin nazari kan illolinsu ko kuma akasi ga lafiyar jama'a, duba da yadda nau'ukan abinci da nomansu akayi ba ko kiwo ke samun ƙarbuwa a wasu kasashen duniya.…
  continue reading
 
Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan mako tare da Khamis Saleh ya mayar da hankali ne kan nasarar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta El-Kanemi Warriors ta lashe kofin kalubale na Najeriya na shekarar 2024. A karshen watan da ya gabata ne dai ƙungiyar ta Jihar Borno ta samu nasarar lashe kofin kalubale na Najeriya, bayan da doke Abia Warriors da ci 2 - 0 a fili…
  continue reading
 
A cikin shirin na wannan mako, zamu sake yin waiwaye kan korafe-korafen makallata fina-finan Hausa, kan yadda mashirya fina-finai suka fi mayar da hankali kan soyayya, tare da fatali da sauran fannonin rayuwa. Za mu tsallaka Jamhuriyar Nijar, inda zamu duba yadda zamani yayi tafiyar ruwa da wake-waken ‘yan mata da ke tashe a baya. Muna tafe da tatt…
  continue reading
 
Shirin duniya kamar yadda aka saba na duba manyan labaran da suka faru a sassan duniya A cikin shirin zaku ji cewa.............. Gwamnatin Najeriya ta sanar da shirin janye biyan kudaden haraji kan wasu muhimman kayayyakin abinci da ta dage haramcin shigar da su kasar, don saƙaƙawa jama’a raɗaɗin tsadar raywar da suke ciki. Matakin sojojin da suka …
  continue reading
 
Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya mayar da hankali ne kan rayuwar fitaccen mawakin gargajiya na jamhuriyar Nijar Alhaji Ali na Maliki Mawakin haifafffen kauyen Sarkin arewa dake jihar Maradi a Jamhuriyar Nijar ya kwashe shekaru akalla 80 na rayuwar sa yana taka rawa a fagen na raye-raye da kade-kaden gargajiya. Shirin ya kuma yi waiwaye ka…
  continue reading
 
Shirin awannan mako zai maida hankali ne kan gasar Firimiyar Najeriya ta NPFL da aka kamala, ta kakar 2023 2024, gasar da Enugu Rangers ta lashe. To kamar yadda kuka ji tuni kungiyar Enungu Rangers ta lashe gasar Firimiyar Najeriya ta bana da aka kammala, yayin da kungiyar Remo da Enyimba suka kasance a matakin na biyu dana uku To tun bayan kammala…
  continue reading
 
Allah ya halici wannan duniya tamu da koguna da dazuka wadanda ke taimako ga rayuwar dan Adam ta hanyoyi da dama. A matakin Nigeria, Allah ya albarkace ta da manyan gandun dazuzzuka da suke da fadi da girma, wadanda suka kunshi nau’o’in tsirrai da mabanbantan dabbobi, wadanda ba a samun su a dazuzzukan da ke wasu yankunan duniya. Amma wasu daga cik…
  continue reading
 
Shirin 'Kasuwa akai Miki Dole na wannan makon ya maida hankali kan yadda gwamnatin Jamhuriyar Nijar, ta fara saidawa talaka shinkafa a farshi mai rahusa, domin saukakawa ƴan kasar radadin matsin tattalin da suke ciki sakamakon juyin mulki da sojoji suka yi. A ranar 26 ga watan Yunin da ya gabata gwamnatin Nijar ta hannun ma’aikatar kasuwanci ta kad…
  continue reading
 
Cikunan ƴan siyasa sun ɗuri ruwa a Faransa, bayan da masu tsattsauran ra’ayi suka lashe sama da 33% na ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen shiga Majalisar Dokokin Ƙasar, tare da yiyuwar samun gagarumar nasara a zagaye na biyu na zaɓen da za a yi ranar Lahadi mai zuwa. Ana matuƙar nuna fargaba dangane da abin da zai faru matuƙar masu wannan ra’ayi suka samu…
  continue reading
 
Shirin al'adun gargajiya na wannan mako, ya je jamhuriyar Benin musaman yankin Wemewe, inda ƙabilar yankin ke shirya wani ƙasaitaccen bikin nuna al’adunsu a duk shekara, wadda ke ƙarfafa danƙon zumunci tsakaninsu da sauren ƙabilu. Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin...By RFI Hausa
  continue reading
 
A wannan mako, shirin ya yi duba ne a kan yadda hare-haren ‘yan ta’adda suka kassara harkokin ilimi a arewacin Najeriya, shekara 10 kenan da 'yan ta'adda suka fara kai hari kan makarantu a Najeriya, lamarin da ya fara faruwa a shekarar 2014 a makarantar sakandaren ‘yan mata ta garin Chibok da ke jihar Borno a Arewa maso gabashin kasar. Bincike ya n…
  continue reading
 
Shirin wannan zai yi dubi ne kan wani rahoton da ya ce an samu hauhawar amfani da makamashi mai gurɓata muhalli da ma hayaƙin da ke illata muhallai a shekarar 2023. Shirin zai duba tasirin wannan al’amari ga muhalli da ma abin da ake buƙatar ɗan adam ya yi don ci gaba da harkokinsa a cikin wannan sarari na subahana Wani rahoto a kan makamashi da ci…
  continue reading
 
Hukumar Yaƙi da Cututuka Masu Saurin Yaɗuwa a Najeriya, ta ce kawo yanzu adadin waɗanda suka kamu da cutar Amai da gudawa wato Cholera sun kai dubu 1 da 579, kuma tuni 54 daga cikinsu suka riga mu gidan gaskiya. Hukumar ta yi gargaɗi ga jama’a da su kiyaye ta hanyar ɗaukar matakan kariya, domin kuwa tuni cutar ta shiga jihohi 32 na ƙasar. Waɗanne i…
  continue reading
 
Yunƙurin ƙara haraji a kan kayayyakin masarufi, ya haddasa ɓarkewar mummunar tarzoma a Kenya, inda aka tabbatar da mutuwar mutane da dama a jiya labara musamman a birnin Nairobi. Shin ko meye ya yi zafi har wannan tarzoma ta ƙazance tare da samun asarar rayuka da kuma cinna wa wani ɓangare na ginin majalisar dokokin ƙasar wuta? Ko akwai wani darasi…
  continue reading
 
Shirin 'Kasuwa akai Miki Dole na wannan makon ya maida hankali da kan kiranda wasu kungiyoyi suka yi wa gwamnatin Najeriya da ta yi wa Allah ta farfado da harkokin noma da sarrafa manja kamar yadda aka san ƙasar a baya. Kungiyar ɗalibai ta ƙasar ta yi kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya farfado da harkokin sarrafa manja da Allah ya wadata ƙasar…
  continue reading
 
A wannan mako, shirin ya yi duba ne a kan sabuwar hanyar koyarwa, da kuma tasirin da ta ke da shi a harkar ilimi a faɗin duniya, wato Innovative Teaching Method a turance. Ita dai sabuwar hanyar koyarwa wato Innovative Teaching Method, hanya ce da ta sha bambam da hanyoyin koyarwa da aka saba gani a lokutan baya, domin ita ana koyar da ɗalibai ne b…
  continue reading
 
Loading …

Quick Reference Guide