RFI Hausa public
[search 0]
More
Download the App!
show episodes
 
Artwork
 
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.
  continue reading
 
Artwork
 
Shirin yakan duba yadda kasuwanci da tattalin arizikin kasashen duniya ke ciki. Kana yakan ji sabbin dubaru da hanyoyin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masana’antu dangane da halin da suke ciki.
  continue reading
 
Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.
  continue reading
 
Shirin Mu Zagaya Duniya na duba Wasu Muhimman Labarai da suka ja hankalin Duniya a cikin mako. Ana gabatar da shirin ne a ranar Asabar da safe a kuma maimaita ranar Lahadi da daddare.
  continue reading
 
Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Jumma'a da safe.
  continue reading
 
Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-daban na duniya, tare da nazari kan irin ci gaban da aka samu wajen binciken kimiya da fasaha da ke neman saukakawa Dan’adam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Bil’adama. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe, a ku maimata ranar Alhamis.
  continue reading
 
Shirin Al’adu, kida da fina-finai, shiri ne da ke zo maku a ranakun assabar da kafe 5:30 na yamma, tare da maimaici da karfe 8:00 na safiyar ranar Lahadi.Inda muke kawo ma ku rahotanni da labaran da suka shafi Fina-finai na gida da ketare, firarraki da mawakammu na gargajiya da na zamani, tare da kawo maku labaran da suka shafi al’adummu na gida da ketare. Tare da naku Mahaman Salisu Hamisu.
  continue reading
 
Shirin Dandalin Siyasa, yana tattaunawa tare da tafka muhawar kan al’amurran siyasa da ke faruwa a kasashen duniya, da batutuwan da suka shafi al’umma kai tsaye, wanda Bashir Ibrahim Idris ke jagoranta. Wannan Shirin na zuwa ne a karshen mako Ranar Assabar da maimaci a ranar Lahadi a Shirye Shiryen Safe da Yamma.
  continue reading
 
Fili ne na musamman kan Fina-finai ta hanyar tattauna da masu ruwa da tsaki a wannan fanni a duniya, Tare da wayar wa ma su sauraro kai da kara masu basira dangane da hikimar da Allah ya bai wa wasu ta fanin shirya fim ko tsara wasan kwaikwayo. Wanda ke zo maku a duk ranar Asabar da safe, tare da maimaici a ranar Lahadi da yamma.
  continue reading
 
Loading …
show series
 
Daga cikin labarun da shirin wannan makon ya ƙunsa akwai harin da wani matashi a Kano ya kaiwa Masallaci ta hanyar cinna masa wuta, wadda zuwa lokacin gabatar da wannan shiri aka tabbatar da salwantar rayukan mutane 15 daga cikin akalla 30 da ke cikin Masalacin. Shirin na kuma ɗauke da tattauna wa da tsohon gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamiɗo, kan tun…
  continue reading
 
Shirin 'Kasuwa akai Miki Dole na wannan makon tare da Ahmad Abba ya maida hankali ne kan matakin gwamnatin Najeriya bukatar masu sana'ar POS da sauran masu mu'amala da na'urar da su garzawa hukumar rajistan kamfanoni ta kasar domin yin ragista kafin ranar 7 ga watan Yulin wannan shekara ta 2024.By RFI Hausa
  continue reading
 
Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya yi tattaki ne har Kanon Dabo da ke tarayyar Najeriya, inda ya yi duba a kan yadda Maza da Mata suka rungumi sana'ar Rini a Karofin Kofar Mata wadda ke da dogon Tarihi. Shirin ya samu zarafin tattauna wa da Baballiya Hamisu, wanda shi ne mai magana da yawun Marinar ta Kofar Mata.…
  continue reading
 
A wannan makon shirin zai yi duba kan cutar kyanda ko kuma measles a turance, cutar da galibi akan ga bullarta a irin wannan lokaci da ake fama da matsanancin zafi musamman a yankunan kasashen yammacin Afrika Sahel. Zuwa karshen watan Fabarairun da ya gabata, fiye da yara 700 suka harbu da cutar kyanda a jihar Borno cikin watan yayinda zuwa yanzu t…
  continue reading
 
Ƙungiyar Ƙwadago da sauran kungiyoyin farar hula a Najeriya sun yi fatali da matakin gwamnati na baiwa bankuna umarnin fara cirar harajin kashi 0.5 wato rabin ɗaya kenan cikin 100, kan duk hada-hadar aika kudaden da ‘yan kasar ke yi ta intanet. A cewar gwamnatin za a rika amfani da sabon harajin don samar da tsaro daga barazanar masu yi wa mutane k…
  continue reading
 
Shirin na wannan mako zai yi dubi ne akan yadda al'ummar karamar hukumar Obagi na jihar RIVERS dake yankin NIGER DELTA tarayyar Najeriya suke fama da matsalar yoyon iskar gas sanadiyar fashewar bututun da aka samu tun a watan Yunin shekarar 2023 wanda yayi sanadiyyar gurbacewar ruwan sha, wanda ya sa al'ummar ke kamuwa da cutar amai da gudawa har z…
  continue reading
 
Daga cikin batutuwan da shirin wannan lokaci ya waiwaya akwai, watsin da kungiyar kwadagon Najeriya ta yi da karin albashin ma’aikatan da gwamnatin kasar ta yi. Sai kuma matakin Burkina faso na rufe karin kafafen yada labarai bisa rahoton da suka bayar na kisan fararen hula sama da 200 da sojoji suka yi. A Kenya kuwa Ambaliyar ruwan ce ta lakume ra…
  continue reading
 
Shirin Lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda al’ummar yankin arewacin kamaru ke fuskanta matsalar rashin tsaftatacce kuma wadataccen ruwan sha ba, wanda ke haddasa gagarumar matsala ga lafiyar mazauna yankunan, wannan shi ne maudu’in da shirin na wannan mako zai mayar da hankali akai. Tsaftatacce …
  continue reading
 
Bayan kammala ziyarar kwanaki biyu da ministar harkokin wajen ƙasar ta kai a Najeriya, gwamnatin Japan ta ce za ta bayar da gudun mowa domin yaƙi da ayyukan ta’addanci a yankin Sahel. A tarihi dai ba kasafai Japan ke shiga batutuwan da suka shafi yaƙi da ta’addanci ba a duniya, abin da ya sa wasu ke ganin cewa duk wani tallafi da zai fito daga ƙasa…
  continue reading
 
Shirin kasuwa akai miki dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya mayar da hankali kan matakin hukumar da ke yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annti EFCC na kaddamar na farautar tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello da kuma binciken wasu tsoffin mukarraban gwamnatin da ta shude kan cin hanci da rasha da kuma rufta da ci da dukiyar al’umma. A Najer…
  continue reading
 
Ƙasashen duniya da kuma ƙungiyoyi kaƙƙin aikin jarida da kuma ‘yancin bayyan ra’ayi, sun yi tir a game da matakin rufe wasu kafafen yaɗa labarai da gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso ta dauka. Baya ga kafafen yada labaran Faransa ciki har da RFI da kuma France24, matakin rufe kafafen yaɗa labaran ya shafi na Amurka, Birtaniya Faransa da dai sauran…
  continue reading
 
Shirin Kasuwa A Kai Miki Dole a wannan makon ya maida hankali ne kan batun korafin ‘yan Najeriya ke yi game da rashin ganin sauyi a farashin kayan amfanin yau da kullum, bayan karyewar farashin ƙudaden ƙetare masamman dalar Amurka da sanadin tashin ta ne ya haddasa mummunan tashin farashin kayayyaki a kasar, wanda har hukumar ƙididdiga ta ƙasar ta …
  continue reading
 
Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon ya maida hankali ne kan yadda wasannin matakin kwata finals na gasar zakarun Turai su ka gudana. A makon da ya gabata ne dai aka kammala wasannin zagayen, inda aka fafata a wasanni 4. Dortmund da aris Saint-Germain da Bayern Munich da Real Madrid ne suka kaiga wasan kusa da na karshe a gasar ta bana. A yanzu B…
  continue reading
 
Daga cikin labarun da shirin karshen makon ya waiwaya akwai neman tsohon gwamnan jihar Kogi yahya Bello da hukumar EFCC ke yi ruwa a jallo, lamarin da ya kai ga daukar matakin dakile duk wani yunkurinsa na ficewa daga Najeriya Shirin ya kuma leƙa gabas ta tsakiya inda Iran ta ƙi fusata kan makamai masu linzamin da na’urorin tsaron sararin samaniyar…
  continue reading
 
Wata kungiyar kare hakkin dan adam ta kasa da kasa da ake kira Global Rights ta bayyana cewa yankin arewa maso yammacin Najeriya shi ne mafi fuskantar ayyukan ta’addanci masu alaka da kashe-kashe ko garkuwa da mutane idan an kwatanta da yankin kudancin kasar. Rahoton da ya bayyana halin da ake ciki a yankin na arewa maso yammacin Najeriya da wani l…
  continue reading
 
A farkon wannan makojn ne yakin da ake gwabzawa a Sudan tsakanin sojojin kasar karkashin Janar Abdel Fattah al-Burhan da kuma dakarun RSF da ke karkashin Mohamed Hamdan Dagalo ke cika shekara guda. Rikicin da aka faro a ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2023, ya yi sanadiyar rasa rayuka da dama da kuma raba miliyoyi da muhallansu, wanda a yanzu MD…
  continue reading
 
Shirin a wannan lokaci ya fi karkata akalar ne kan gasar Firimiyar Ingila, wadda ke ci gaba da jan hankali, duk da shawo gangarar da akayi. Yar manuniyar dai tuni ta fada kan kungiyoyin ukun saman tebur, wato Manchester City, Arsenal da Liverpool, lura da yadda suke kan kan kan a yawan maki, abunda ke kara nunawa duniya yadda gasar ta Firimiya ta k…
  continue reading
 
Yayin da aka cika shekaru 10 da sace dalibai a makarantar sakandiren 'yan mata da ke garin Chibok a jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya, har yanzu akwai matan kusan 100 da ke tsare a hannun mayakan Boko Haram da suka yi garkuwa da su. Gwamnatin kasar dai na ci gaba da ikirarin cewa, tana iya bakin kokarinta wajen ganin an sako sauran 'yan ma…
  continue reading
 
Masu sauraro daga sashin Hausa na RFI cikin shirin Mu Zagaya Duniya da saba zabo wasu daga cikin muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya gabata, domin bitarsu. A ranar Larabar da ta gabata al'ummar Musulmin Najeriya suka bi sahun takwarorinsu na duniya wajen gudanar da Sallar Idi Karama, wadda aka saba gudanarwa bayan kammala azumin …
  continue reading
 
A wannan makon Shirin Duniyar Wasanni ya yi duba ne kan yadda ake tufka da warwara game da tsarin tsaro a lokacin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics da birnin Paris zai karbi bakunci a watan Yulin wannan shekarar. Shire-shiryen gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta Olympics da birnin Paris na Faransa zai karbi bakunci a watan Yuli mai zuwa sun…
  continue reading
 
Shirin a wannan mako zai ba da hankali ne akan tsananin zafin da ake fama da shi a wasu yankuna na Nahiyar Afirka, a wannan shekarar ya tsananta inda a wasu sassa na tarayyar Najeriya lamarin ya dan wuce misali. Jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya, jiha ce da tun asali aka sani da tsanantar kowane juyin yanayi na Zafi ko na Sanyin Hunturu ko ma na…
  continue reading
 
Kasa da shekara guda bayan rantsar da sabbin gwamnonin Najeriya, 13 daga cikin su, sun ciyo bashin da yawan sa ya kai dala biliyan 2 daga kasashen waje ko kuma cibiyoyin bada lamuni daban-daban. Cin bashi a tsakanin gwamnatocin Najeriya ba sabon abu bane sai dai kuma abinda ‘yan kasar ke fargaba shine idan har an ciyo wannan adadin bashi a kasa da …
  continue reading
 
Shirin Kasuwa a Kai Miki Dole a wannan makon ya maida hankali ne kan kananan sana’o’i da matasa ke yi don samun na abinci a lokacin azumin watan Ramadana a Damagaram da ke jamhuriyar Nijar. wasu daga cikin sana'oin da matasan sukafi mai da hankali akai dai sun hada da bredi ko kayan marmari ko kayan lambu da dai sauransu. Ku latsa alamar sauti don …
  continue reading
 
A ranar Talata ne aka rantsar da sabon shugaban kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye, wanda ya lashe zaben kasar a makon da ya gabata da kaso sama da 54 cikin 100 na yawan kuri’u sama da miliyan 7 da aka kada. Faye shine shugaba mafi kankantar shekaru a Afrika, kuma ya lashe zaben ne a wani yanayi da kasar ke cikin chukumurdar siyasa. Matashin ya z…
  continue reading
 
Kiristoci a fadin duniya su na gudanar da bukukuwan Easter, ranar mai mahimanci da ke zagayowa duk shekara don tunawa da sadaukarwar da Isa Almasihu ya yi domin duniya, wadda a cikin sakon Paparoma Francis yai kira ga duniya bisa kiyaye afkuwar yaki kowanne iri. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.…
  continue reading
 
Shirin a wannan mako shirin ya yi sharhi ne kan kamun ludayin mai rikon kwaryar tawagar Super Eagles ta Najeriya Finidi George, bayan da tawagar ta buga wasannin sada zumunci biyu a makon daya gabata karkashin kulawar Finidi George da aka damkawa tawagar a hannunsa a matsain mai horaswa na rikon kwarya. Tawagar ta yi nasara kan takwararta ta Ghana …
  continue reading
 
Loading …

Quick Reference Guide