Best cikin podcasts we could find (Updated June 2017)
Related podcasts: Islamic Religion Education Shiga Falalar Musulinci Malan Fatawan Zarri Ummu Musulmai Hadisin Ummar Daga Akidodin Idodi Aljani Ibadatillah Jamiau Idodinsa  
Cikin public [search 0]
show episodes
 
Y
Yadda aljani yake shiga cikin mata
Daily+
 
Malam yayi bayani yadda aljani yake shiga cikin jikin dan adam da kuma musamman yadda yake matsama mata . sannan wajibine ga musulmi yayi imani da samuwar aljannu kamar yadda allah yaffadeso acikim alkur’ani Yadda yake macama mata a harkokinsu nayau da kullun da kuma dalilanda ke kawoso da kuma hanyoyinda magan cesu karkashin alkur’ani da sunna annabi(saw)
 
H
Hukumcin bawali cikin rowan da basa gudu da alwala ko wanka acikinsu
 
Malan yayi bayanine akan Hukumcin yin bawali cikin rowan da basa gudu da alwala ko wanka acikinsuTareda cewa bai halittaba kuma idan rowan masu yawane basu canza launinsaba ko tdan tdanonsa ko iskansa ya halitta amma idan basuda yawa bai halittaba ayi alwalla ko wanka a cikinsu.Da wasu hukumce hukumne masu alaka dashi wanda wajibine musulmi yasansu.
 
S
SHAFA LABARI SHUNI
Monthly+
 
A wannan shiri, muna karanto littafan Hausa masu ma’ana, musamman na da can, irin wadanda aka dade da wallafa su domin su tuna mana rayuwa, da al’adunmu na Hausawa kafin zuwan Turawa da ma bayan zuwansu. A cikin littafan akwai hikimomi, da dabaru, da almara, da kuma abubuwan ban mamaki, da na ban sha’awa da birgewa, da jaruman marubutan suka yi.
 
L
Ladubban shiga ban daki
Daily+
 
Malan yayi bayanine akan Ladubban shiga ban daki da kuma ladubban biyan bukata a cikin daji da cukin gari Dakuma bayani akan anfiso musulmi ya zamanto koda yaushi cikin tsalki tareda cewa rishin tsanki baya cikin zuhudu Da wasu hukumce hukumne masu alaka daladubban biyan bukata wanda wajibine musulmi yasansu.
 
T
Tafsirin surar yusuf
Daily+
 
Surar tana karantar da halayen rayuwar mutun a cikin duniya tareda abokan zama a kowane matsayi da sauransu
 
H
Hukuncin aske kai batarada auzuriba
 
Malan yayi bayanine akan aske gashinnkai taredacewa yin haka sifface daga cikin siffofin yan bidi a amma yahalitta askeshi gawandakeda waniciwo akansa ko wani lalura akansa .
 
S
Sharhin Al jamiau fi ibadatillah
 
Abindake wajibi akan kowane musulmi yasansu daga cikin nau aukan ibada dakuma wasu kura kuran da wasu musulmai kefatdawa acikinsu, da fadakarwa akansu.
 
L
Lokacin suhur da fa idodinsa a ramadan
 
Malan yayi bayayi akan faIalar yin sahur a cikin azumi da kuma lokuttan yin sahur, wanda yakamaci ko wane musulmi ya sansu domin azuminsa yayi dai dai da sunna annabi
 
H
Hakkokin mace a musulunci
Daily+
 
Musulunci yazo domin yabaiwa mata hakkokinsu,domin shine wanda yagirmama mata , kuma ya kwatu musu hakkinsu, daga ckin hakkokinsu a musulunci shine yatabbatammata rishin banbanci tsakaninta da namiji wajan aikata ibada , da kuma bata sakamako wajan allah. Daga cikin hakinta bata zabi wajan yimata aure, hakinta akan mijinta.kamar ciyarwa shayarwa.
 
Z
Zikirin safe da marece
Daily+
 
Zikirinda akeyi da safe da kuma marece ,kuma yana daga cikin yima allah madaukaki bauta sannan ana ambaton allah da baki kuma ana ambatonshi da gabubuwa na jiki.dagacikin fa idodinshi yana karama zuciya haske kuma yana kankaremata tsatsan zunubi. kuma zikiri yana kore shedan.
 
B
Bidi a acikin addinin musulinci
Daily+
 
Kaset na(1) ma anar bidi "a acikin addini da kuma sanin mahimmacinta dakuma sanin ma anar dukkan bidi a batacce koda mutane suna ganinta keikkiawace da kuma ma anarsa aharshan larabci tareda dalilai kan haka. Dagacin abinda ke jawowa allah baya karba kuwane aiki wanda za a samu lada sannan duk wanda yakoyi dan bid a yanada kamishon laifinsaKaset na(2)sabubbanda kekawo kirkira bidi a cikin addinin musulunci da kuma hadarinda ke cikin bidi a da kum nisantar yan bidi a.
 
F
Fa idodi daga hadisin ummu zarri
 
Wanna hadisi na ummu zarri , wanda uwarmu a isha matar manzon allah take bada labarinshi ga annabi da kuma matansa, daga cikin fa idodin wannan hadisi bayani akan yadda miji zai zamo,namiji nagari mai cautatawa matarsa , dagacikin fa ida wannan hadisi kuma samun kekkiawan zama
 
F
Falalar matayan manzon allah (asw)
Daily+
 
Bayanin falalar matayan annabi muhamad cira da amincin allah sutabbata gareshi da iyalan gidansa da kuma matsayinsu wajan musulmi kuma yimusu biyayya yana dagacikin imani kinsu da kin yimusu biyayya kafurcine sannan baya halitta musulmi ya auri samada mata hudu yanadaga cikin abinda manzon allah yacce, sannan muyi koyi da gidan annabi yadda yake zaman takewa da matansa akan kautatawa.
 
F
Falalar Sha’aban da kuma bidi’o’in dake cikinsa
 
Malamin ya yi bayanine akan falalar watan Sha’aban, da kuma yadda musulmi ya kamata ya kasance a cikinsa, sannan ya yi bayanin halayan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi da kuma halayan magabata a cikin watan, da kuma bidio’in da ake yi a watan.
 
A
Akidodin al ummar musulmai
Daily+
 
Malam yayi bayani kan bidi،a acikin addini , yakuma banbanta stakanin bidi،a da sunna ta manzon allah (saw). bidi،a bata kasancewa sai a cikin addini ba acikin lamurran duniyaba , san yanuna hadarin bidi a ,yakoma bada misali kan bidi،a acikin addini,sannan yattabo akidar yan shi’a da kuma hadarisu kan ahli sunna, sannan akarshe yayi bayani kan yan kur’ani .
 
F
Fatawan malan jafar
Daily+
 
– 1- Tambatoyoyi a kan azumin sofaffi da hukuncin munafurci , da hukuncin shan taba , da sauransu .– 2- Hukuncin sallah bayan da bidi a , da hukuncin zuwa kasuwa ga mace ,da kuma hukuncin musulmi ya auri kirista ko bayahudiya , da suransu .– 3- Hukuncin kadaituwa da mace kafin auranta, da hukuncin maulidi , da hukuncin sakin mace cikin haila , da sauransu.– 4- Hukuncin kadaituwa da mace kafin auranta, da hukuncin maulidi , da hukuncin sakin mace cikin haila , da sauransu.– 5- Hukuncin mu a l ...
 
T
Tarbiya a musulinci
Daily+
 
Malan yayi bayani ne akan mahimmacin tarbiya a musulinci da kuma mahimmacinta acikin al aumma Yayi bayani akan hayyoyin da addini musulinci yasamuna wajan yiwa yara tarbiya Tare da cewa tarbiya tanason sa idon iyaye akan yaransu saboda tarbiya an ginatane akan soyayya tsakanin yara da iyayensuYana daga cikin hakkokin yara akan iyayensu samusu son allah a zukatarsu dakuma sauran mahimma darussa masu alaka da tarbiya wanda wajibine kowane musulmi yasansu
 
D
Dankonzumunta a addininmuslunci
Daily+
 
Mahimmacin yan uwantaka acikin addin musulinci da kuma sada zumunta acikin addinin musulunci,musulmai yan uwan junane yana da cikin imanin mutum musulmi bayacika sai yasoma danuwa abidayakesomakansa na alkairi. Sanan musulmi bayacutar damutane shine kuma janhankullaan yin karatu da karantarwa da kira dayinwaazi. Mututamutum da girmamashi kuma yafadakarda tuna niimomin da allah yayima musulmi shine aikowar dan sako zuwa garemu shine annabi muhamad (saw) dagacikin niimomin da allah yayimuna sh ...
 
Loading …
show series
 
Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen sama ta Najeriya NCAA, ta bukaci kamfanonin layukan sadarwa da sauran masu ruwa da tsaki, kan sufurin jiragen sama, da su nemi izini kafin tsawaita gine-ginensu ko kafa turakunan sadarwa. A cikin wata sanarwa da ta fitar, hukumar ta bayyana muhimmancin mutunta wannan tsari da ta ce, yana kunshe a cikin dokar ...…
 
Duk da matakan da Hukumomi daban-daban suke dauka domin hana ratsa Sahara don zuwa Turai, har ya zuwa wannan lokaci wasu na ci gaba da sai da rai domin wannan tafiya mai hatsari. Ko da a dan tsakanin nan, an sami hasarar rayukan wasu bakin haure dake neman tafiya wasu kasashe amma saboda rashin ruwan sha suke rasa rayukansu. Wasu bayanai na nun ...…
 
A cikin ‘yan makwannin baya-bayan nan ana yawan samun hare-haren Boko Haram musamman a wasu yankuna da ke cikin jihar Borno, yayin da wasu ke bayyana fargaba kan yadda ‘yan Boko Haram ke afka wa mutane idan suka fita zuwa gonakinsu. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya tattauna da Alhaji Muhammad Mustapha Maikanuri.…
 
T
Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare
 
Cikin wannan shiri Tattaunawa da Ra'ayoyin masu sauraro wanda Zainab Ibrahim ke gabatarwa za'a ji yadda musulmi suka yi Karamar Sallah.
 
A cikin shirin mu zagaya Duniya Mahaman Salissou Hamissou ya dubo wasu daga cikin manyan labaren da suka maida hankali zuwa yaki da ta'adanci a yankin Sahel.
 
Cikin wannan shiri wanda Nura Ado Sulaiman ke gabatarwa za'a ji illolin amfani da takin zamani da aka gurbata shi.
 
Cikin wannan shiri da Hauwa Kabir ke gabatarwa za'a ji tattaunawa da wani fitaccen gwani ta harkan kwalliya a Fim. Akwai kuma hira da wani gwani ta fannin wake-wake dake zaune a Zaria.
 
Shirin ya tattauna game da kasuwancin shinkafa a Najeriya, wadda ke daya daga cikin kayan abincin da ‘yan kasar ke kuka da tsadar farashinsu , musamman shinkafar yar gida da ake nomawa a arewacin kasar.
 
Malaman Addinin Islama sun bukaci al’ummar Musulmin duniya da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukan alheri musamman a cikin goman karshe na watan azumin Ramadan da ke dab da karewa. Malaman sun bayyana goman karshen a matsayin mafi muhimmanci fiye da sauran ranakun watan na Ramadan. A game da muhimmancin goman karshen, Abdurrahman Gambo Ahmad ...…
 
Sarki Salman na Saudiya ya nada dansa Muhammad Bin Salman a matsayin yarima mai jiran gado, matakin da ya sauya tsarin gidan sarautar kasar. An nada Muhammad bin Salman ne a matsayin Yarima bayan tube Muhammad bin Nayef wanda kuma aka sauke daga kujerar Ministan cikin gida. Wannan dai na a matsayin karin karfi ga sabon Yariman wanda ya yi watsi ...…
 
Cikin wannan shiri na tattaunawa da jin ra'ayoyin jama'a za'a ji abinda jama'a ke cewa dangane da zaben wakilan majalisar Dokokin kasar Faransa da aka gudanar karshen mako.
 
Kungiyar Matasan Arewacin Najeriya, ta rubuta budaddiyar wasika, zuwa ga mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Osinbajo, inda ta bukaci ya baiwa masu fafutukar kafa kasar Biafra, damar yin hakan cikin lumana.Cikin wasikar da kusoshin kungiyar biyar suka sa hannu, sun yabawa kokarin mukkadashin shugaban, na tattaunawa da kowane bangare don warwa ...…
 
Cikin wannan shiri da Hauwa Kabir ke gabatarwa na Dandali Fasahar Fina-finai za'a ji tattaunawa da tayi da gwanin shirin Fim Faisal Munniru da ake kira Golden Boy.
 
Kamar yadda ya alkawalta a lokacin yakin neman zabensa shugaban kasar Amruka Donald Trump ya sanar da dakatar da duk wata yarjejeniyar hada hadar kasuwanci tsakanin kasar da Cuba, sakamakon yarjejeniyar da Barack Obama ya cimma da shugaban Cuba Raul Castro a 2014.salissou Hamissou ya duba wasu daga cikin manyan labarai na mako a cikin shirin Mu ...…
 
Shirin kasuwa a kai miki dole na wannan tare da Awwal Janyau ya tattauna ne kan korafin 'yan kasuwa a Nijar, da suka ce wasu cibiyoyin hada-hadar kudad ko kuma kanana bankuna da ke ba su rance sun yi awon gaba da kudadensu, lamarin da ya jefa 'yan kasuwan cikin damuwa musamman masu karamin karfi.
 
A kokarin da take yi na karkata akalar samar da kudadenta daga bangaren man fetur, gwamnatin Najeriya ta bude wani taron zuba jari a bangaren hakar ma’adinai, wanda ya janyo masu zuba jari daga sassan duniya. Domin sanin tasirin shirin da kuma yadda zai taimaka wa kasar, Bashir Ibrahim Idris ya tattaunawa da Alh. Yusuf Datti Yahya, daya daga ci ...…
 
Yau shekaru 24 ke nan da gudanar da zaben shugabancin kasar da aka yi ranar 12 ga watan yunin 1993, zaben da ake cewa Cif Moshood Abiola ne ya lashe amma sojojin da ke kan karagar mulki karkashin jagorancin janar Ibrahin Badamasi Babangida suka soke sakamakonsa. An dai sha gudanar da tarzoma domin ganin an tabbatar da Abiola a matsayin shugaban ...…
 
Cikin wannan shiri Hauwa Kabir ta tattauna da gwanin harhada wakoki cikin Fim wato Aliyu Sulaiman Raf-Demon.
 
Cikin wannan shiri Garba Aliyu Zaria ya tattauna da manoman shinkafa a jihar Kebbi dake Najeriya game da kokarin su na ganin sun ciyar da Najeriya da abinci.
 
Sakamakon zaben wakilan majalisar kasar Birtania na nuna cewa Jamiyyar Conservative ta Firaminista Theresa May ba ta sami rinjaye a Majalisa ba wanda suke bukata domin aiwatar da kudurorin Jamiyar.Duk da gaza samun rinjayen dai Firaministan ta bayyana cewa za ta kafa Gwamnati da niyyar ganin sun sami aiwatar da manufofin sun a ficewa daga cikin ...…
 
Shirin Kasuwa a kai miki dole na wannan makon tare da Awwal Janyau ya kai ziyara ne kasuwar 'yan lemu da ke jihar Kano a Najeriya, in da ya tattauna kan rahusar da aka samu a hada-hadar kayayyakin marmari a cikin wannan wata na Azumin Ramadan. Kasuwar ta kuma hada 'yan kasuwa da ke safara daga kasashen Afrika.…
 
Shirin al'adunmu na gado na wannan makon tare da Nura Ado Sulaiman ya tattauna ne kan al'adar neman aure a kabilar Mumuye. A cikin shirin za ku ji abubuwan da al'adar ta kunsa tun daga neman auren har zuwa tarewa a gidan miji.
 
A Talatar nan ce ake cika shekaru 50 da fara yakin Israila da falasdinu a shekarar 1967, yakin da ya haifar da kafa kasar Israila da kuma daidaita Falasdinawa, da tare da mamaye wasu Yankunan Falsdinawan da Isra'ila ta yi a waccan lokaci zuwa yanzu. Bikin cika shekaru 50 din na zuwa ne a daidai lokacin ake kokwanton samun kasar Falasdinu sakama ...…
 
Cikin wannan shiri na Dandalin fina-finai wanda Hauwa Kabir ke gabatarwa za'a ji hira da wani fitaccen dan Fim da ya hada harkan Fim da malanta, sannan kuma za'a ji tattaunawa da wani fitaccen mai sai da fina-finai a Najeriya.
 
Cikin wannan shiri da Garba Aliyu Zaria ya gabatar za'a ji irin kokarin da manoma a jihar Kebbi ke yi domin ciyar da Kasar da abinci. Akwai tattaunawa da Sarkin Noman Jihar Kebbi Alhaji MUhammadu Hakimi Jiga wanda ya ce yana ganin ya kyautu ya zama Sarkin Noman duk Duniya.
 
Shirin ilimi hasken rayuwa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris, ya ci gaba ne daga in da ya tsaya a makon jiya, in da ya tattauna kan kere-keren kayayyaki daban-daban da wani matashi mai suna Muhammad Auwal Mele ya yi a Najeriya. A cikin shirin na wannan makon za ku ji yadda jirgin da wannan matashi ya kera ya tashi sama tare da yin ya ...…
 
Shirin al'adunmu na gado na wannan makon tare da Nura Ado Sulaiman na wannan makon ya dora ne daga in da ya tsaya a makon jiya kan bikin al'adar farautar Belle a cikin al'ummar Mumuye a jihar Taraba da ke Najeriya.
 
A
AWR Hausa - هَوْسَ
 
Prayer and Humility-Kaskanci cikin Adua / It pays to be kind- Mu kasanci da ayuka AlheriBy podcasts@awr.org (AWR).
 
Cikin wannan shiri da Garba Aliyu Zaria zai gabatar za'a ji yadda manoma a jihar Kebbi dake Najeriya suka amsa kiran da Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi cewa a koma noman shinkafa gadan-gadan.
 
Daga cikin muhimman labaran da shirin Mu Zagaya Duniya na wannan lokacin ya sake dubawa akwai batun ziyarar da shugaban Amurka Donald Trump ya kai kasar Saudiya, inda ya halarci taron kasashen Muslmi. Zalika shirin yana kushe da wasu manyan labarai ko al'amuran da suka auku a sassa daban daban na duniya a akon da muka yi bankwana da shi.…
 
Cikin wannan shiri Hauwa Kabir ta tattauna da wasu fitattun jarumai a fannin fina-finai a Najeriya.
 
Shirin Ra'ayoyin Masu Sauraro na wannan lokacin ya bayar da damar tofa albarkacin baki ne kan matakin da gwamnatin Jihar Kano ta dauka na janye binciken da ake wa masarautar Kano, karkashin jagorancin majalisar dokokin jihar, bisa zargin cewa masarautar barnatar da biliyoyin kudi cikin dan karamin lokaci.…
 
A cikin shirin dandalin fasahar Fina-Finai Hawa Kabir ta samu zantawa da wasu yan wasan Fim dake arewacin Najeriya dangane da irin kalubale da suke fuskanta.
 
Cikin wannan shiri na Mu Zagaya Duniya wanda Salissou Hamissou ke gabatarwa akwai batun badakalar kutsen Komfutoci a kasashen duniya masu dama na duniya.
 
Shirin na yau ya bai wa masu sauraro damar tofa albarkancin bakinsu ne kan halin da ake cikin a kasar Cote d'Ivoire's, inda tsaffin 'yan tawaye kuma sojin kasar a yanzu, suka shafe kwanaki suna bore bisa wasu hakkokinsu da suke neman gwamnatin kasar ta biya su.
 
A jiya lahadi 14 ga watan Mayu aka soma gasar cin kofin kwallon kaffa na yan kasa da shekaru 17.a karawar farko Guinee ta doke Gabon da ci 5 da 1,Ghana ta doke Kamaru da ci 4 ba ko daya.A cikin shirin, Abdoulaye Issa ya duba mana irin kokarin da hukumomin Nijar suka yi wajen kasasncewa a Gabon.
 
A Jamhuriyar Nijer, Jihar Diffa dake gabashin kasar na daya daga cikin wuraren da ke kan gaba wajen fama da matsalar sare saren itace tsakanin shakaru biyu zuwa uku, a wannan karon dai sabuwar sana’ar saran itacen ta bulla ne kasancewar dubban ‘yan gudun hijira da suke cikin sansani a wajen garin, wadanda rikicin kungiyar boko haram ya raba da ...…
 
Cikin wannan shiri na Mu Zagaya Duniya Salissou Hamissou ya duba mana batun nasarar zaben Shugabancin Faransa inda Emmanuel Macron ya yi nasara.
 
A cikin shirin dandalin fina -finai Hawa Kabir ta samu tattaunawa da wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a harakar Fina-finai tareda ambato wasu daga cikin matsalollin da suke fuskanta.
 
A
AWR Hausa - هَوْسَ
 
Isaac and Rebeccah, the family that trusted in God. Ishaku da Matarsa Rebeka, iyali da sun dogara ga Allah / Making the right choices in life. Zabi mai kyau a cikin rayuwa / You are responsible for your Choices-kada ka ba wani laifiBy podcasts@awr.org (AWR).
 
A cikin shirin Fina -finai Hawa Kabir ta dubo hanyoyin da masu tsara Fina -finai a Najeriya ke amfani da su domin shirya fim da ma irin kalubalen da suke fuskanta.
 
Cikin wannan shiri na Mu Zagaya Duniya za'aji sharhi game da ranar 'yan jaridu ta duniya da kuma wasu bayanai dangane da zaben kasar Faransa.
 
Speed
Series preference
1x
1x
Volume
100%
/

Google login Twitter login Classic login