Gwamnatin sojin Nijar ta kwaɓe wa Bazoum rigar kariya
Manage episode 423695505 series 1237821
Daga cikin Labarun da shirin ya waiwaya a wannan mako akwai matakin mahukuntan sojin Jamhuriyar Nijar na cirewa hamabararren shugaban ƙasar Bazoum Muhd rigar kariyar, abinda ya bude kofar samun damar gurfanar da shi gaban kotu.
A Najeriya kuwa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce zai ci gaba da yi wa tattalin arzikin ƙasar garambawul duk kuwa da yadda hakan ke ta’azzara wahlhalun da al’ummar kasar ke sha.
Sai Kuma Senegal inda shugaban kasar Basirou Diomaye Faye ya sassauta farashin kayayyakin masarufi don saukaka wa jama’a tsadar rayuwar da suke ciki.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanar da ƙaruwar mutanen da rikici ke tilastawa barin matsugunansu a sassan duniya, adadin da zuwa yanzu ya kai mutum miliyan 120.
24 episodes